Wata 'yar Najeriya mazauniya Amurka ta bayyana cin amanar da wani dan uwanta ya mata bayan ta dawo gida Najeriya ta tarar gidan da ta ke turo masa kudi domin a gina mata bai kammala ba.
Matar, wadda ta ce ta tura masa kudi sama da naira miliyan hamsin domin ginin wannan gida, ta ce sama da shekara arba'in ta shafe a kasar tana kwadago.