Dalibi ɗan shekara biyu ya mutu bayan faɗowa daga benen makaranta

Iyaye sun shiga halin jimami yayin da ɗansu mai shekara biyu da wata shida ya faɗo daga ginin makaranta ya rasu a garin Aba da ke jihar Abia cikin kwanakin nan.

Alfijir Labarai ta rawaito rahotanni sun ce yaron mai suna David Udo, ɗalibin makarantar ‘Emerald International School’ da ke kan titin ‘Crystal Park’, Aba, ya faɗo daga saman bene mai hawa uku na makarantarsu. An garzaya da yaron asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

A cewar iyayen yaron, wasu mutane ne da ba su sani ba suka kira su a wayar tarho suka shaida musu abin da ya samu yaron nasu a makaranta.

Mahaifin yaron mai suna John Udo wanda lauya ne ya yi zargin cewa har zuwa ranar Asabar shugaban makarantar bai kira su ya faɗa musu abin da ya faru da yaron nasu ba.

Da BBC ta tuntubi shugaban makarantar , Peter Nwoke, ya ce rahotonnin da aka bayar ba daidai ba ne, amma ya ki yin wani karin bayani kan abin da ya sani a kan lamarin. “Ba abin da ya faru ba ke nan,” in ji shi. “Idan kun zo ido da ido zan bayyana muku abin da na ji ya faru saboda ba na nan abin ya faru.”

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Maureen Chioma Chinaka, ta shaida wa BBC cewa an samu korafi daga iyayen yaron kan abin da ya faru, kuma rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

Kalli Video Kaitsaye Anan 👇



Post a Comment

Previous Post Next Post