Tirkashi! CBN nazargin Anbuga Jabun Sabbin Kudaden N200, N500, N1000

 Kwanakin kada da fara amfani da sabon kudin na N1000 da N500 da kuma N200, bayanai sun ce an fara samun jabun Naira dubu daya da ke yawo a tsakanin 'yan kasar.

Yan Najeriya sun fara yin tambayoyi kan ko an fara yin jabun wasu daga cikin sabbin kudin kasar.

Wannan dai na zuwa ne bayan bullar wani faifan bidiyo a kafafen sada zumunta, inda wani mutum yake kokawa kan yadda wani ya bai wa matarsa da ke sana’ar POS jabun sabuwar naira dubu daya da babban bankin kasar ya kaddamar ranar 15 ga Disambar da muke ciki.

A bidiyon mijin matar ya nuna jabun naira dubu dayan da ta gasken, ta yadda al’umma za su bambance su.


Yadda za ku gane jabun sabon kudin

Sabon kudin dai na dauke da wasu lambobi na tsaro da za su saukaka maka gane jabun da mai kyau.

Babban bankin Najeriya ya yi bayani a shafinsa na intanet game da yadda mutane za su gani sabon kudin na gaske da jabu, da ka gan su ko ka rike su a hannu.  

“Abubuwan da suka bambanta su su ne launinta da kuma yadda take idan ka rike ta a hannu, da irin tsaron da aka sanya mata da tambarin da ke jikinsu.

CBN ya ce kalar da aka kara wa kudin wani nauyi ne na tsaro da saukin gane na gaske da jabu.

Kazalika zaren tsaro da ke jikin kudin, za ka ga kamar an rarrabe suke, amma ba a raba su ba, idan ka ga kudin a haske za ka ga akwai rubutun CBN da aka yi shi kanana a gaba da bayan kudin.

Haka kuma babban bankin Najeriya ya ce rubutu da ke jikin kudin da lambobin da ke jiki an kara musu kauri.

Kalli Cikakken Bidiyon👇👇👇👇


Sannan babban bankin ya ce sabon kudin na da wani tsaro ta yadda ba za a iya kwafin sa ba.

Dukkan wadannan alamu da babban bankin ya ambata, babu su a jabun sabuwar dubu daya, 500, da 200.

A cewar babban bankin Najeriyar masu samar da jabun kudin ba su da masaniyar wadannan matakan tsaron da sabon kudin ke dauke da su.

Yadda Babban Bankin ke sakin kudin.


Post a Comment

Previous Post Next Post