Amarya Ta Shararawa Uwar Mijinta Mari A Akan Abincin Biki.

 Innalillahi 🙆😭😳

Kwana biyu bayan daurin aure, wani ango ya nemi saki saboda rashin da’ar da amaryarsa ta yi wa mahaifiyarsa

Matarsa da mahaifiyarsa sun yi rikici a wajen liyafar aurensu wanda ya sanya har suka shararawa juna mari

Ya tubure ya ki daukar shawarar mahaifiyarsa ta ya dauki dangana, angon ya nace cewa sai ya datse igiyar auren da ke tsakaninsa da amaryar

Auren kwana biyu kacal ya tunkuyi dutse bayan da sabon angon ya shigar da kara neman saki bisa rashin daraja mahaifiyarsa da matarsa ta yi.

Wani fan Najeriya wanda ya karanci ilmin dabbobi, Abdullah A Abdullah, wanda ya wallafa labarin ya bayyana cewa da gaske ya faru sannan ya nemi shawara daga wajen masu amfani da yanar gizo.

Abdullah ya bayyana cewa fushin da angon ya yi ya samo asali ne biyo bayan wani abu da ya faru a wajen liyafar auren shi, wanda ya sanya matarsa da mahaifiyarsa suka mari juna.

Lamarin ya faru ne bayan wasu baki daga bangaren mahaifiyar angon sun iso wajen basu samu abinci ba ya kare. Ragowar abincin da amaryar ta ajiye domin iyayenta ne kawai ya yi saura.

Mahaifiyar ta sa sai ta tunkari amaryar inda ta rada mata cewa ta taimaka ta dan debo mata daga cikin abincin ta ba bakinta saboda bai dace ba idan aka bari suka koma ba tare da sun sanya wani abu a cikinsu ba duba da sun zo daga nesa ne.

Nan fa amaryar ta shafawa idon ta toka ta ki yarda inda tace abincin iyayenta za ta ba. Bayan ta bata baki ta ki yarda, sai mahaifiyar tasa ta sanya kwano ta debo abincin da kanta amma sai amaryar ta kwace ta mayar da shi cikin kula.

Cikin fushi sai uwar mijin ta shararawa matar danta mari, wacce ita kuma ta sanya hannu ta rama. Abdullah ya ce mijin ya samu labarin abinda ya faru inda ya ki daukar mataki a wajen sai bayan kwana biyu ya nemi saki a kotu.

Abdullah ya ce ana ta shari’ar sakin sannan angon ya ki sauraron hakurin da mahaifiyarsa ta ba shi na ya manta da komai kawai ya yafe matar tasa.

Kalli Video Kaitsaye Anan 👇

Post a Comment

Previous Post Next Post