EFCC Kano Ta Damƙe Tsohon Shugaban KASCO Da Ɗansa Kan Batan Biliyan 4

 Hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta kama tsohon Manajan Daraktan Kamfanin samar da taki na jihar Kano (KASCO) Bala Muhammad Inuwa, kan zargi da laifin karkatar da sama da Naira biliyan 4 mallakin gwamnatin jihar Kano.

Alfijir Labarai ta rawaito hukumar ta fara binciken batan kudaden gwamnati a kamfanin samar taki na Kano (KASCO) da suka haura Naira Biliyan hudu tare da kwace wasu motoci da manyan motoci da taraktoci na noma.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kabir Abba Kabir mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ya fitar ranar Alhamis, a Kano.

An kama su ne bisa zargin karkatar da dukiyar jama’a, da kuma yin kalaman karya ko kuma dawo da sama da Naira biliyan 4 da gwamnatin jihar Kano ta warewa kamfanin samar da taki na Kano (KASCO) a matsayin tallafi. In Ji sanarwar.

Hakazalika hukumar na tsare da dan tsohon Manajan kamfanin Bala Inuwa Muhammad , wanda ya rattaba hannun a madadin mahaifinsa, tare da karkatar da kudaden da suka kai N3, 275,685,742.00 ta hanyar asusun ajiyar wata kungiya dake da jigista da hukumar yiwa kamfanoni rijista CAC.

“Haka kuma an karkatar da kudaden da suka kai Naira Miliyan 480 ta asusun ajiyar banki na wani kamfanin kasuwanci mai suna ‘Limestone Processing Link’ wanda yake karkashin jagorancin mai waccan kungiya, Inda aka yi amfani da shi wajen tura naira miliyan 400 zuwa asusun banki mai suna Bala Muhammad Inuwa.

Sanarwar ta kara da cewa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.


Kalli Cikakkiyar Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post