Ƴan Bindiga Sun Kashe Malaman Sakandare 2 Da Raunata Mataimakin Shugaban Makarantar

 Wasu ‘yan bindiga sun kashe malaman makarantar sakandare biyu tare da raunata mataimakin shugaban makarantar Beco Comprehensive High School dake jihar Fulato

Alfijir Labarai ta rawaito Kakakin kungiyar Berom Youths Moulder-Association (BYM), Rwang Tengwong wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, ya ce an kashe wadanda harin ya rutsa da su ne a ranar Litinin a lokacin da ma’aikatan makarantar ke gudanar da wani taro a shirye-shiryen gabatar da jawabi da ranar bayar da kyaututtuka, wanda aka gudanar ranar Juma’a.

Kungiyar ta zargi wasu makiyaya da kashe malaman, inda ta bayyana cewa sun bude wa ma’aikatan makarantar wuta ne a lokacin da aka ce su bar harabar makarantar a yayin da ake taron.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, bai sami damar amsa kiran da wakilinmu ya yi kan lamarin ba har zuwa hada rahoton.

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka samu munanan raunuka a makarantar da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, 2023.

Ma’aikatan sun bukaci makiyayan da su fitar da shanunsu daga muhallin makarantar.

Amma maimakon su bi, sai suka fito da makamai suka bude wa malaman wuta.

“Hakan ya yi sanadiyar mutuwar ma’auratan da suka yi aure kwanan nan, Rwang Danladi da matarsa, Mrs Sandra Rwang Danladi, wadanda ma’aikatan makarantar ne yayin da Mista Dalyop Emmanuel Ibrahim wanda shi ne mataimakin shugaban makarantar ya samu munanan raunuka, yanzu haka yana jinya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos-JUTH.” In Ji kakakin kungiyar.

Amma da aka tuntubi shugaban kungiyar ci gaban Fulani ta Gan Allah a jihar, Garba Abdullahi, ya musanta zargin, inda ya ce ba Fulani makiyaya ne suka yi kisan ba, ya kara da cewa makiyayan ba sa kiwo a kusa da makarantar, yana mai kira ga jami’an tsaro da su binciki lamarin da kuma fitar da wadanda suka aikata wannan aika aika.

Sai dai kungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta hana kiwo a fili a jihar.


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇

Post a Comment

Previous Post Next Post