Alƙaliyar Tirabunal Ta Koka Kan Wani Lauya SAN Bisa Yunƙurin Bata Cin-Hanci

 Duk wanda ya karɓi kuɗi a madadina, Allah zai hukunta shi da shi da zuri’arsa har ma da waɗanda ba a haifa ba.

Alfijir Labarai ta rawaito shugabar kotun sauraron kararrakin zabe ta Majalisar Tarayya da ta Dokoki q Jihar Kano, Mai shari’a Flora Azinge, ta bayyana fushinta kan yunkurin wani babban Lauya mai muƙamin SAN, na neman ya ba ta cin hanci.

Alkaliyar da ta ke jawabi gabanin fara zaman sauraron ƙararraki a ranar Talata a Kano, ta koka kan yadda manyan lauyoyi musamman ke aikata wannan mummunar dabi’a .

Ko da ya ke ba ta bayyana sunan babban lauyan ba, Ms Azinge ta ce SAN ɗin da ake magana a kai na da shari’a a gaban kotun.

Babban Lauyan Najeriya da ke da shari’a a gabana ya na kokarin ba ni cin hanci.

Tun jiya kudi ke yawo a wannan kotun.

Duk wanda ya karɓi kuɗi a madadina, Allah zai hukunta shi da shi da zuri’arsa har ma da waɗanda ba a haifa ba. In Ji ta.

“Suna ci gaba da zagin alkalai, suna zagin mu kullum a cikin jaridu, a kafafen yada labarai – cewa muna karbar rashawa.

Bari in sake jaddada muku cewa kada kowa ya sake tunkara ta da cin hanci Na gamsu da abin da Allah ya ba ni, kuma ina da rufin asiri,”

Sai dai Eyitayo Fatogun, SAN, wanda ya kasance a gaban kotun, ya tsaya a madadin dukkan lauyoyin da suka halarta, kuma ya bukaci alƙaliyar da ta kai ƙorafi ga hukumomin da suka dace.

Domin karfafa hujjar sa, babban lauyan ya ce ya ga inda shari’o’in da ake tuhumar alkalan da suka kasa gabatar da kararraki na irin wannan dabi’a ta cin hanci.

Kalli Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post