Ibtila’i: Jerin Gawarwakin da Cutar Sanyi ‘Diphtheria’ Ta Kashe Mutune 80 A Najeriya – NCDC

 Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa cutar Diphtheria ta barke a Babban Birnin Tarayya Abuja inda mutum daya ya kamu sannan ta yi ajalin mutum daya dan shekara hudu a watan Yuni.

Alfijir Labarai ta rawaito wata takarda da hukumar ta fitar ranar Alhamis ya nuna cewa mutum 798 sun kamu da cutar a kananan hukumomi 33 dake jihohi takwas da Abuja a watan Disembar 2022.

Zuwa yanzu cutar ta yi ajalin mutum 80 a Najeriya.

Diphtheria ta fi kama yara kanana a Najeriya.

NCDC ta bayyana cewa cutar ta fi yaduwa a jihohin Kano, Lagos, Yobe, Katsina, Cross River, Kaduna da Osun.

Hukumar ta ce kashi 71.7% daga cikin mutum 798 din da suka kamu da cutar yara ne ƴan shekara 2 zuwa 14.

NCDC ta yi kira ga iyaye da su kai ‘ya’yan su ana yi musu allurar rigakafi domin samar musu kariya.


Cutar Diphtheria

Cutar Diphtheria cuta ce da kwayoyin cutar bacteria mai suna ‘Corynebacterium’ ke haddasa ta.

Cutar ta fi kama yara da manya musamman wadanda ba su yi allurar rigakafin cututtuka da ake yi wa yara ba.

Cutar kan kama makogoro, hanci sannan wasu lokuta fatar mutum.

Cutar ya fi yaduwa idan ana yawan zama kusa da wadanda suke dauke da ita, idan mai dauke da cutar ya rika yin tari ko atishwa a tsakanin mutane.

Alamun cutar sun haɗa da zazzabi, yoyon hanci, ciwon makogoro, idanu su yi jajawur, tari da Kumburin wuya.

Wasu lokuta mai fama da cutar zai rika ganin wasu farin abubuwa na fitowa a kusa da makogoron sa wanda ke hana mutum iya yin numfashi.


Hanyoyin samun kariya daga cutar

  1. Yin allurar rigakafi
  2. Saka takunkumin fuska musamman idan za a shiga cikin mutane.
  3. Toshe baki da hanci idan za a yi tari ko atishwa.
  4. Tsaftace muhalli, wanke hannu da ruwa da sabulu a kowani lokaci.
  5. Zuwa asibiti idan aka kamu da zazzabi ko idan ba a gane lafiyar jiki ba.

Kalli Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post