GANGANCI KO JAHILCI ne Ihun da mutane ke yi kan tsadar litar man fetur a Najeriya, Ahmed Ilallah

 Babu abin da ya haɗa gwamnati da tashin farashin litar man fetur ko kuma saukar sa, a yau a yadda a ke ciki a Najeriya babu ruwan biri da gada.

Gwamnatin Najeriya, tun farkon hawan wannan Gwamnati ta Bola Ahmed Tinubu, ta yi dacen jefar da mangwaro ta huta da kuda.

Amma abin takaicin, wanda kuma zai ba kowa mamaki, shine yadda mutanen da bai kamata su yi ihu ba akan wannan batu suke ihu, hadda masu ruwa da tsakin da su aka kafa dokar Man-Fetur ta kasa, wato PIB, irin su Kungiyoyin Kwadago, har da ma Yan Majalisun Dokokin mu na kasa, wanda a wannan zauren ne a kayi dokar.

Wannan doka ce ta haramta bada tallafin Man-Fetur, kuma ta amincewa kasuwa ta yi hallinta a kan duk farshin da ya danganci al’amuran Man-Fetur a Nijeriya.

Ya kamata mu fa sani, ko kuma mu sake tunawa cewa, a dokokin Kasar Nijeriya a yanzu da suka danganci saye da sayarwar Man-Fetur da dangogin su, babu ruwan Gwamnati ta sanya baki wajen kayyade firashin sa.

A Nijeriya a yau muna kan tafarki ne na Kasuwa ta yi halinta ne, kamar yadda Bature yake kira Perfect Market, ko kuma Capitalism inji masu pilosafar kasuwanci.

Abin kunya ne a ce, har majalisar dokoki sun gabatar da kudiri, rage kudin man fetur da yayi tashin gwauran zabi har zuwa sama da N600, wanda a nazarin tattalin arzikin wannan kasa, wannan soma tabi ne, domin tsarin saye da sayar da Naira a Nijeriya, har yanzu bai daidai ta ba, kuma a na harsashe tashin kudin Gurbataccen Danyan Man-Fetur a duniya.

A wannan Majalissar ne ga a ka yi dokar PIB, ta sami sahalewar Shugaban Kasa, ta zama PIA a 2022.

Kadan da ga abin da zamu fahimta a game da dokar Man-Fetur ta kasa (Nigerian Petroleum Act (PIA) 2021, game da farashin Man-Fetur.

Dokar PIA ita ce ta samar da dukkanin tsare-tsare da sharudda ta yadda za a gudanar da duk wani al’amura da suka shafi Fetur a Nijeriya. Ita wannan doka ita ce ta baiwa shugabanni da gwamnati kafa ta rabewa a kan babu ruwanta da farashin Man-Fetur, kawai kasuwa ce zata yi halinta. Wannan doka ta soke wasu hukumomin NNPC irin DPRR, Petroleum Equalization Funds.

Wannan doka ce ta ta canja kamfanin NNPC (Nigerian National Petroleum Cooperation) zuwa kamfani mai zaman kansa wato NNPC Limited, ya zama mai neman riba kamar kowane kamfanin ‘Yan-Kasuwa, kuma yana biyan haraji.

A cikin tanaje-tanajen wannan Doka, bayan wata shida da sakawa wannan doka hannu, kasuwace zata na kayyade farashin Man-Fetur, sabo da haka maganar bayar da tallafi ta wuce.

Duk da cewa Gwamnatin baya ta Shugaba Buhari ta kara lokaci kafin cire tallafin, har zuwa karshen wa’adin ta, amma sabon Shugaba Tinubu ya karasa tabbatar da cire tallafin.

Ganganci ko Jahilci ne, ya kamata mu tuna fa cewa, kafin Majalisa ta 9 karkashin jagorancin Senator Ahmed Lawal da Femi Gbajabiamila su yi dokar Man Fetur ta kasa wato PIB, wannan dokar ta shafe shekaru 20 a majalisar dokokin kafin yin ta a 2022.

Abin mamaki ne a ce wani Dan Majalisa ya tashi ya kawo Kudurin rage farashin Man-Fetur, shin bai san wannan doka ba, da abin da ta tanada ba

Abin mamaki ne a ce wani Dan Majalisa ya tashi ya kawo Kudurin rage farashin Man-Fetur, shin bai san wannan doka ba, da abin da ta tanada ba?

Hatta su kansu kungiyoyin kwadago, ya kamata su san tanaje tanajen wannan doka, da kuma sanin bamu da wata mafita a kan tilastawa gwamnati shiga lamarin firashin Man-Fetur, har sai an gyara wannan doka.

Babban kuskuren da masana suka hango kafin wannan doka, kusan shi ke faruwa a yanzu,

Gwamnati ta gaza samar da abubuwan da zasu taimaka wajen aiki da wannan doka ba tare da ‘Yan Nijeriya sun shiga wannan galabaitar ba.

Shekaru sama da ashirin da yin aniyar wannan dokar, har yanzu gwamnati ta kasa samar da matatun Man-Fetur a Nijeriya, Gwamnati ta gaza bawa yan kasuwa damar samarwa, ko a samu saukin nemo canjin Dalar Amurka.

Saboda haka, walau ganganci ko jahilci ne, ke samu ihun a kan tashin farashin man fetur.

Kalli Video Kaitsaye Anan 👇

Post a Comment

Previous Post Next Post