GAREKU MASU ƁATA 'YA'YAN MUTANE
Muna gab da tauna tsakuwa don Aya taji tsoro a kowane lokaci ga duk mutumin da Hukumar Hisbah Board Sabon Gari ta kama dumu dumu da matar wani ko Ɗiyar wani a hotel suna alfasha.
Komai Girmanka ko matsayin ka a gari haka zalika kema macce komai Girmanki ko kankantarki, Zamu watsa hotunan ku a Shafukan mu na yanar gizo.
Ba zamu lamunci duk masu lalata 'ya'yan mu, kannenmu da matan mu ba a faɗin karamar hukumar Sabon Gari.
Don haka maɓarnata a kiyaye🤷🤷
20-07-2023