NDLEA Takamo Wiwi Da'akayi Odar su Zuwa Arewa Saboda Sallah 🙄 Jirgin Ruwa Makare

NDLEA Ta Kama Jirgin Ruwa Makare Da Tabar Wiwi A Lagos. Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da NDLEA ta fitar a ranar Lahadi.

Ta bayyana cewa bayan samun bayanan sirri, jami’anta sun yi kwanton bauna a kan hanyar Epe zuwa Lekki da safiyar Litinin inda suka tare wata babbar mota dauke da wasu manyan buhunhunan wiwi da nauyinsu ya kai kilo 2,434.1 a cikin motar.


Kalli Video Firan da Simogala ɗin Kaitsaye Anan 👇


ta rawaito hukumar ta fara kamen ne a kan hanyar Epe zuwa Lekki inda daga bisani jami’an hukumar da ke aiki a cikin teku suka yi kame a Alpha Beach da ke Jihar Legas.

Ba tare da bata lokaci ba direban motar ya yi tsalle ya fito daga motar inda ya gudu a cikin wata mota kirar hilux wadda ke yi wa motar wiwin rakiya.

Hakazalika sanarwar ta ce a kamen na biyu, jami’anta da ke aiki a cikin teku ne suka yi shi, bayan sumun bayanan sirri, inda suka kama wani jirgin ruwa dauke da tabar wiwin da nauyinta ya kai kilo 2,910 a kusa da bakin ruwan Alpha kafin wanda ya fito daga Ghana.

Hukumar ta ce an kama wasu ‘yan kasar Ghana da suka hada da Monday Saba mai shekara 30 da kuma Hakeem Kwana mai shekara 27.

A Jihar Edo da ke kudancin Nijeriya kuwa,

Sanarwar ta ce jami’an nata sun far wa dajin Ekudo da ke Karamar Hukumar Uhunmwode a jihar Edo, inda suka lalata sama da kadada biyu ta tabar wiwi.

Hukumar ta ce bayan lalata gonar ta wiwin, sai da ta gano kilo 67 na tabar.

Video 👇



Ta kara da cewar, ta kama mutum shida bisa zarginsu da hannu a noman wiwin wadanda suka hada da Onyeka Onyedinma da Monday Onyedi da Alex Eboh da Edosa Imariagbe da Godbless Tunde da kuma Godstime Osarobo.

Post a Comment

Previous Post Next Post