EFCC Ta Kame Wani Sanatan Bogi Kan Damfarar Makudan Kudi

 EFCC ta kama wani sanata na jabu, Ifechukwu Makwe bisa zargin zamba cikin aminci ta intanet €5.7m.

Alfijir Labarai ta rawaito an kama Makwe ne a unguwar Guzape da ke Abuja, biyo bayan wasu sahihan bayanan sirri kan ayyukan damfarar sa ta intanet.

Wata sanarwa a ranar Litinin ta Shugaban sashin wayar da kai da kafofin sadarwa Wilson Uwujaren ta fitar, ya ce mayaudarin ya damfari wani dan kasar Spain ta hanyar amfani da sunaye daban-daban.

“Bayan kama shi, an gano cewa wanda ake zargin mai suna da yawa (Fahad Makwe, Sanata Tompolo, Tom Makwe, Dr. Bran), ya damfari wani dan kasar Spain kudi Yuro miliyan 5.7.

Makwe ya yi ikirarin cewa shi ma’aikaci ne na Hukumar Bincike ta Amurka, wakilin FBI, kuma lauyan diflomasiyya kuma ya yi nasarar damfarar wanda aka zambatar ta hanyar amfani da bayanan karya.

Sanarwar ta kara da cewa wanda ake zargin ya fara damfarar mutumin ne a shekarar 2013 a lokacin da ya fara haduwa da ita a shafukan sada zumunta.

Uwujaren ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.


Video Kaitsaye Anan 👇🙆


Post a Comment

Previous Post Next Post