Ma’aikatan Banki Sun Kashe Matar Wani Customansu

 Jami’an ‘yan sanda reshen jihar Ogun sun kama wasu jami’an bankin Micro Finance su huɗu da laifin kashe wata mata ‘yar kimanin shekara 50.

Marigayiyar ta kasance matar ɗaya daga cikin kwastomomin bankin ce kuma hakan ta faru ne a lokacin da suka je gidan su bisa kokarin karɓo bashin kudin da mijinta ya karɓa.


Kalli Cikakken Video Kaitsaye Anan 👇


Matae mai suna Vivian Omo, wanda ake zargin ɗaya daga cikin ma’aikatan bankin ne mai suna Ajibulu, wanda a halin yanzu ke hannun yan sanda, ya ture ta wanda wannan yayi sanadiyar mutuwar ta har lahira, yayin da sauran huɗun: Badmus Olalekan, Ajibade Oludare, Eniola Aduragbemi da Femi Oloko suma suka shiga hannu wajen jami’an tsaro dake garin Ifo na jihar Ogun, inda lamarin ya faru.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce a lokacin da marigayyar ke ƙoƙarin hana jami’an bankin sai ɗaya daga cikinsu mai suna Ajibulu ya ture ta ta faɗi kasa, daga nan ne ta sume aka garzaya da ita asibitin da ke kusa don duba lafiya.

Daga baya Likitan da ke bakin aiki ya ayyana ta “ta mutu bayan isowarta”.

Sai dai lamarin ya tilastawa ɗiyar marigayyar gaggawar kai kara ga ‘yan sanda a hedkwatar shiyya ta Agbado, wanda hakan ya sa jami’in ‘yan sanda mai kula da harkokin ‘yan sanda CSP Awoniyi Adekunle, ya jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa wajen da lamarin ya faru an kuma samu nasarar kama jami’an bankin su huɗu.

An ajiye gawar marigayyar a babban ɗakin ajiye gawawwaki na babban asibitin.

Oyeyemi ya kuma bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olanrewaju Oladimeji, ya bayar da umarnin miƙa waɗanda ake zargi sashen kisan kai na hukumar binciken manyan laifuka da leken asiri ta jihar wato sashen (SCIID) don tsaurara bincike.

Post a Comment

Previous Post Next Post