Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 1, Sun Harbe Mutum 2 A Jihar Kano

 Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani mutum mai shekaru 60 a duniya tare da harbe wasu biyu a kauyen Gangarbi da ke karamar hukumar Rogo a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda, ​​ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Kano ranar Talata.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 1:30 na safe.

Ya ce ‘yan sandan sun samu labarin ne da misalin karfe 01:30 na safe, cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki kauyen Gangarbi da ke karamar hukumar Rogo inda suka yi awon gaba da wani Alhaji Na’ayya Gangarbi zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Dauda ya ce, nan take rundunar hadin gwiwa ta jami’an sintiri na sashen, JTF da kuma masu yaki da masu garkuwa da mutane suka garzaya wurin.Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa an kwashe wasu mutane biyu da suka samu raunukan harbin bindiga – Maskuru Ukaisha a kafarsa ta dama da Salisu Ibrahim a kafadarsa ta hagu, inda aka garzaya da su babban asibitin Rogo domin samun kulawa.

A cewarsa, an tura karin jami’an tsaro dauke da makamai zuwa yankin domin bibiyar ’yan bindigar da duk wasu bata-gari da ke kawo cikas ga zaman lafiya a tsakanin mazauna yankin.“Jami’an tsaro dauke da makamai da sauran tawagogin dabara tare da ‘yan banga an tura yankin domin samun nasarar ceto wadanda abin ya shafa,” inji shi.

Kalli Cikakken Video Kaitsaye Anan



Ya ce an fara gudanar da bincike domin kamo wadanda suka sace tare da kubutar da wadanda abin ya shafa.

Post a Comment

Previous Post Next Post