Hukumar EFCC Ta Damke Wasu Masu Sana’ar POS Mutum 80

 EFCC ne suka cafke awasu ma’aikatan PoS 80, Sakamakon sayar da Naira a kan kudi da ya haura hankali a Akure, babban birnin Jihar Ondo.

Hukumar ta kai harin bisa rahoton sirri kan zargin saye da siyar da kudade ga wasu masu ruwa da tsaki. An kai harin ne a kananan hukumomin Akure ta Kudu da Akure ta Arewa.

An tattaro cewa an tilastawa ma’aikatan PoS bayyana inda suka samo kudaden da su ke kasuwancinsu dasu.

Wata majiya ta ce wasu jami’an PoS sun amsa cewa sun sayi kudi daga bankuna bayan sun caji kwastomominsu.

A cewar majiyar: “Sun kama ma’aikatan PoS kusan 80 a yankin Oja Oba.

Ta kara da cewa, idan sun zo wurin ku, za su nemi ku bayyana inda kuka samo kuɗin, da kuma nawa kuke cajin abokan cinikin ku, sannan kuma su nemi ku kai su wurin wanda ya ba ku kuɗin.

“Wasu ma’aikatan PoS, wadanda suka samu bayanin tun da farko, sun ranta a na kare abin su.


Kalli Cikakken Video Kaitsaye 👇 Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post