An Harbe Kansila Barawon Akwati _ Ansamu Nasarar Harbeshi ne Jiya da Dare ALokacin Kirgan Kuri'u

An Harbe Kansila Barawon Akwati _ Ansamu Nasarar Harbeshi ne Jiya da Dare ALokacin Kirgan Kuri'u

Rahotanni daga jihar Kano na cewa an harbe wani tsohon kansila a bisa zarginsa da sace akwatin kaɗa ƙuri'a.

Lamarin ya faru ne a yayin da ake gudanar da zaben gwamna da na 'yan majaliasar dokokin jiha a ranar Asabar É—in nan.

Rahotannin sun ce sojoji ne suka harbe Ibrahim Nakuzama, wanda tsohon kansila ne a mazaɓar Getso da ke ƙaramar hukumar Gwarzo.

Sai dai kawo yanzu rundunar sojan Najeriya ba ta kai ga fitar da sanarwa kan lamarin ba.

Wani makusancin mamacin ya ce tuni aka yi jana'izarsa a mahaifarsa a Getso.

Makusancin ya ce suna cikin jimamin rashin Ibrahim din, don haka babu wani bayani da zai ƙara. Ibrahim Nakuzama ya rasu ya bar mata biyu da ƴaƴa shida.

Ita ma a na ta É“angaren, rundunar Æ´an sandan jihar Kano ta ce ta kama mutane da dama saboda zargin tayar da hankali a lokacin zaben na ranar Asabar.


Ku kalli Cikakken Video Kaitsaye 👇 Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post