Ministoci Sun Amince Afara Koyawa Yan Kannywood Karatun Hausa a Aji

 Majalisar ministoci ta gwamnatin Najeriya ta amince da wata manufa kan amfani da harsunan kasar wajen koyar da dukkan daliban kasar a matakin firamare a fadin kasar.


Ministan Ilimi Adamu Adamu ne ya sanar da haka ga manema labarai, bayan taron majalisar ministoci da aka yi a ranar Laraba cewa majalisar ta amince a aiwatar da sabon tsarin amfani da harsunan gida da ake kira National Language Policy wanda ma’aikatarsa ta kirkiro

Ministan ya bayyana cewa ” ka'idojin koyarwa na shekaru shida na farko a makaruntun firamare za su kasance cikin harshen gida.”

Tun kafin Najeriya ta samu 'yancin-kai daga Birtaniya take amfani da Ingilishi a matsayin harshen hukuma inda cibiyoyin ilimi a kowa ne mataki suke amfani da shi a matsayin harshen gama-gari na koyarwa.

Haka kuma wasu al’ummomi na amfani da harsunan gida tare da Ingilishi a azuzuwa. A yanzu mahukunta sun ce za a fi ba harsunan gida fifiko a makarantun firamare.

A cewar ministan ilimin Najeriya: ''Yara sun fi koyon abu da sauri, idan aka koyar da su a cikin yarensu na gida.”

Ministan Ilimin ya amince cewa aiwatar da sabon tsarin na iya zama kalubale domin, “ yana bukatar aiki tukuru wajen samar da kayayyakin koyarwa da malaman da za su yi wannan aiki da sauransu.”


Wani kalubale da za a iya fuskanta shi ne yawan harsunan da ake amfani da su a Najeriya, wadanda sun kai 625 a cewar mahunkan kasar.

Wannan na nufin cewa zabar yarukan da za a yi amfani da su na iya zama wani abu mai wahala a kasar da ta fi yawan al’umma a Afirka.

Ministan ya ce ba za a takaita koyarwar a kan manyan harsuna uku na kasar ba

 ‘’Akwai harsuna 625 a Najeriya kuma idan muka sami kayayyakin koyarwa, za a rika koyar da makarantu da ke kowa ce al’umma da harsunan gida, kuma ba za mu takaita koyarwar ga manyan harsunan kasarnan uku ba wato Hausa da Ibo da na Yarabanci”.

“ Sannan yayin da ake koyar da su darussa cikin harsunan iyayen nasu, za a kuma ba su damar koyon wasu harsunan Najeriya da suke sha’awa, baya ga koya musu manyan harsunan kasa da kasa kamar Turancin Ingilishi da Faransanci da Larabci da sauransu” in ji shi.

Sai dai babu cikakken bayani a kan lokacin da sabon tsarin zai soma aiki.

Mahukuntan ilimi a Najeriya sun ce da farko za su so su fara samar da kayayyakin koyarwa da malaman harsunan na gida kafin shirin ya soma aiki gadan-gadan.

Post a Comment

Previous Post Next Post