Maganar Aure Ta Yi Karfi Tsakanina Da Mustapha Waye Kafin Rasuwarsa, Hajara Izzar So

Aisha Babandi ta tabbatar da cewar akwai maganar aure tsakaninta da marigayi Mustapha Waye kafin rasuwarsa Jarumar wacce aka fi sani da Hajara Izzar So ta ce ta shiga mawuyacin hali bayan samun labarin daraktan saboda shakuwar da ke tsakaninsu Ta ce shine mutum na farko da ya daga darajarta har ta zama wata a rayuwa kasancewar ita marainiya ce ba uwa ba uba 

Fitacciyar jarumar Kannywood, Aisha Babandi wacce aka fi sani da Hajara a cikin shirin ‘Izzar so’ mai dogon zango ta bayyana yadda ta shiga halin wayyo Allah bayan rasuwar babban darakta, Nura Mustapha Waye. 

A wata hira da gidan radiyon Freedom na jihar Kano yayi da ita kuma Mujallar fim ta saurara, jaruma Aisha ta bayyana cewa sun shaku matuka da marigayin don har suna maganar yin aure a tsakaninsu.

Maganar Aure Ta Yi Karfi Tsakanina Da Mustapha Waye Kafin Rasuwarsa, Hajara Izzar So Hoto: aysha_bloody.

Kamar yadda Mujallar Fim ta rahoto, jarumar ta ce marigayin shine mutum na farko da ya taimake ta a rayuwa har ta kai ga zama wata domin dai ita din marainiya ce babu uwa babu uba. Ta ce:

Dama chan muna tare kuma shine mutumin farko da ya taimaki rayuwata har na kai ga zama wata a rayuwa, kasancewar ni marainiyace bani da uwa, bani da uba kuma na tashi ne a gaban yayar mahaifiyata.” Ta kuma bayyana cewa ko mutuwar iyayenta bata ji shi a jikinta kamar yadda ta ji na daraktan ba saboda dama chan ba a gabansu ta taso ba. 

Ta kara da cewa: 

Kasancewar ban yi rayuwa tare da iyaye na ba ya sanya mutuwarsu bata taba ni kamar yadda mutuwar darakta Nura Mustapha Waye ta taba ni ba. 

Akwai soyayya da maganar aure a tsakaninmu kuma har abun ya yi karfi kafin Allah ya amshi ransa, saboda haka na shiga damuwa har ma ban san irin yadda zan kwatanta yadda na ji ba.” Jarumar ta bayyana rashin a matsayin abin da ba za ta manta da shi ba inda tayi masa addu’ar Allah ya jikansa, ya bata makamancinsa. 



Post a Comment

Previous Post Next Post