DA DUMI-DUMI: Ada Eme ta zama Sarauniyar Kyau ta Nijeriya a Shekarar 2022.
Ada Eme, wadda ta fito daga jihar Abia ta lashe kambun The Most Beautiful Girl in Nigeria (MBGN 2022) a jihar Legas ranar Juma'a, kamfanin Silverbird ke shirya gasar duk shekara.
Ada Agwu Eme ta zama mafi kyawun yarinya a Najeriya, MBGN, na 2022.Ada Eme, wanda ya wakilci Miss Abia, ta doke sauran ’yan takara 37 da suka fito daga sassan Najeriya domin neman kambu a daren Juma’a, a Otal din Eko da Suites da ke Legas.
Ada ce za ta wakilci Najeriya a gasar Miss World mai zuwa, yayin da Montana Felix za ta zama wakiliyar Najeriya a Miss Universe.DAGA Saliadeen Sicey