Tsagerun Yan Bindiga sun Kashe Soja da Manoma a Kaduna

 Wasu tsagerun 'yan bindiga sun farmaki wani kamfanin gona a jihar Kaduna sun, hallaka wani soja An sace wasu mutane biyu yayin da 'yan bindiga suka farmaki kamfanin gonan da ke wani yankin jihar 'Yan bindiga sun tasa jihohin Arewa maso Yamma a gaba, ana yawan samun tashe-tashen hankula.

Karamar Hukumar Kubau, jihar Kaduna Dake Nigeria, Rahoton daga jaridar Daily Trust Tana cewa, wasu ‘yan bindiga sun farmaki wani kamfanin gona a Anchau na karamar hukumar Kubau a jihar Kaduna. An ce tsagrun sun yi bindige wani soja tare da yin awon gaba da wasu jami’an kamfanin gonar mutum biyu da misalin karfe 1:30 na ranar Laraba. An tattaro cewa, daya daga cikin wadanda aka sacen wani dan kasar Zimbabwe ne da ke aiki a kamfanin. 

 Cewarsa: 

Sun kashe wani soja da ke aiki a kamfanin na gona tare da yin awon gaba da wani mutumi mai suna Charles Choko dan kasar Zimbabwe da wani Yusuf Aliyu Bello dan jihar Kano. Wani mutumin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa, ya ga tawagar jami’an tsaro a ranar Juma’a tana shiga dajin da ke yankin domin nemo wadanda aka sacen. An kira shugaban karamar kukumar, Basher Suleiman Zuntu, amma ba a same shi ta waya ba. Haka nan, bai mayar da sakon tes da aka tura masa ba. A bangarensa, DSP Mohammed Jalige, ya yi alkawarin nemo cikakken bayani kuma zai tuntubi manema labarai.

Post a Comment

Previous Post Next Post