Budurwa ta wallafa sakonnin Soyayya da mai gadinta ya tura mata a dandalin Whatsapp
Daga Hajiya Mariya Azare
Wata matashiyan budurwa yar nigeriya,Temitope Akinrimisi, ta wallafa sakonnin da mai gadinta ya wallafa mata a whatapp.
Maigadin yafada tarkon sonta tsamo-tsamo,dan haka ya fallasa mata sirrin zuciyan shi ta dandalin zumunta.
Temitapo tace a yanzu bata da sukuni a gida saboda batayi, tsammanin mai gadinta zaifada tarkon sonta ba.
Temitapo tace tacika da mamakin samun sakon soyayya ta whatapp daga mai gadinta
A sakonnin daya wallafa a twitter mai gadin yace ta dade tana burgeshi, amma a yanzu bazai iya cigaba da boye sirrin a cikin zuciyanshi ba.
Ya roketa akan tabashi dama sannan tayi watsi da ganin cewa shi din mai gadi ne.
Da take wallafa hotunan hiransu a twitter temi tace, mai gadina yafada mini yana sona a yanzu banajin inada kariya kuma.