Najeriya Ta Samar Da Motocin Bas-Bas Domin Rage Kuɗin Sufuri A Ƙasar

 Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana Cewa Najeriya zata tura Motocin safa masu rahusa masu inganci a fadin kasar a wani mataki na rage tsadar Sufuri da kuma bunƙasa Tattalin Arzikin ƙasar.

Alfijir Labarai ta rawaito a jawabi da ya yiwa ‘yan Najeriya Domin murnar samun ‘yancin kai, Tinubu ya bayyana cewa Sabbin Motocin bas ɗin zasu yi aiki da dan kadan na man fetur, Wanda hakan zai yi tasiri Ga Farashin Sufuri.

Gwamnatin Tarayya na samar da wuraren bada horo da bita a faɗin ƙasar nan, domin horarsa da samar da sabbin damammaki ga masu zirga-zirga da ‘yan kasuwa.

Samar da motocin bas na CNG abin farin ciki ne da ake sa ran zai yi amfani da damammaki ga Najeriya. In Ji shi.

Ya ƙara da cewa, zai taimaka wajen rage farashin sufuri ga ’yan Najeriya, da kuma saukaka wa jama’a damar zagayawa da kuma samun muhimman kayayyaki da ayyuka.

Wannan yana da mahimmanci musamman Ga Gidaje masu ƙaramin karfi, waɗanda ke kashe adadin kuɗin shigarsu akan Sufuri.

Hakazalika amfani da CNG zai taimaka wajen rage dogaro da Najeriya keyi kan man da ake shigo dashi daga ƙasashen waje, wanda hakan zai sa ƙasar ta samu Kuɗin shiga Motocin bas na CNG wani mataki ne mai kyau ga Najeriya Wanda ake sa ran zai sami fa’ida da dama Ga tattalin arziki da al’ummar ƙasa baki ɗaya


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇



Post a Comment

Previous Post Next Post