Yadda ambaliyar ruwa ta lalata sassan Libya tare da kashe mutane 2000

 Ambaliyar ruwa a ƙasar Libya ta haddasa mutuwar mutane akalla dubu biyu, sannan da dama sun bata bayan wata mahaukaciyar gugguwa dake tafe da ruwan samar kamar bakin kwarya ta ɗaiɗaita yankin gabashin ƙasar.

Alfijir Labarai ta rawaito wakiliyar BBC ta ce tashar jirgin ruwan Derna na daga cikin yankunan da ambaliyar ta fi yi wa illa, inda rahotanni ke cewa madatsun ruwa biyu da gadoji biyu sun ɓalle.

Galibin birnin ya koma karkashin ruwa. An ƙaddamar da dokar ta baci a yankin, tare da ayyana zaman makokin kwanaki uku. A yanzu haka rahotanni na cewa guguwar ta doshi yammacin Masar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Kalli Video Kaitsaye 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post