Gwamnatin Tarayya Ta Kara Farashin Mitar Wutar Lantarki A Najeriya

 Hukumar da ke kula da wutar lantarki ta Nijeriya (NERC) ta amince da karin farashin mitar wutar lantarki da ake biya a kasar.

 Alfijir Labarai ta rawaito wata takardar da shugabannin NERC, Sanusi Garba da Dafe Akpeneye suka sanyawa hannu kuma mai kwanan wata 5 ga watan Satumba, 2023, ta bayyana cewa, mita mai layi daya za a biya Naira N81,975.16 maimakon Naira N58,661.69 da ake biya a baya, sai kuma mita mai layi Uku, za a biya Naira N143,836.10 maimakon Naira N109,684.10

Takardar ta ce, an sabunta farashin ne don tabbatar da daidaiton farashin mitoci ga masu amfani da wutar.


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇

Post a Comment

Previous Post Next Post