Akwai shari’o’i dubu 39,526 a gaban mu – In Ji Kotun Ɗaukaka Ƙara

 Shugabar Kotun Daukaka Kara, Mai Shari’a Monica Dongban Mensen, ta ce kotun daukaka kara na da shari’o’i 39,526.

Alfijir Labarai ta rawaito mai shari’a Mensen ta bayyana haka a yayin bikin kaddamar da sabuwar kalanda shekarar shari’a ta 2023/2024. Ta ce kotun daukaka kara ta samu jimillar kararraki dubu 7,295 da kuma kararraki 3,665 a shekarar 2022/2023.

“A shekarar shari’a ta 2022/2023, an shigar da jimillar kararraki 7,295 da kuma ƙorafe-ƙorafe dubu 3,665 a sassa 20 na kotun.K otu ta kammala kararraki dubu 3,765 sannan ta kori kararraki 5,617.

An kori 1,030 daga cikin waɗannan kararraki kuma an ba da izini a kan 10,381. Har yanzu kotun tana da jimillar kararraki 39,526 da ake sauraro zuwa ranar 31 ga watan Agusta, 2023. Wannan karuwa ce daga dubu 34,037 da ke gaban kotu a shekarar shari’a ta 2021/2022,” in ji ta.

Ta ce an samar da kwamitocin shari’a 98 domin sauraren ƙorafe-ƙorafen zabe a fadin kasar nan domin gudanar da jimillar korafe-korafe 1,209 da aka shigar.

Kalli Cikakkiyar Video Kaitsaye 👇

Post a Comment

Previous Post Next Post