Shanu sunfi min sauƙin kiwo a kan mulkin Najeriya Tshohon shugaba

 Shanuna sunfi min sauƙin kiwo a kan mulkin Najeriya.

Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shanunsa sun fi masa saukin kulawa fi ye da mutuanen Nijeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne a wurin liyafar cin abinci da aka shirya a Abuja gabanin ya koma mahaifarsa ta Daura a ranar Litinin bayan ya mika ragamar shugabancin Nijeriya a hannun, Bola Ahmed Tinubu.

Da yake yabawa da sakamakon zaben 2023, Buhari ya taya ‘yan Nijeriya murnar wajen yin amfani da kuri’unsu domin zaben shugaban da suke bukata.

Tsohon shugaban ya ce babban zaben 2023 ya kasance mai cike da tarihi na bayar da kasar nan turbar dimokuradiyya.

“Na koma mahaifata domin in ci gaba da kulawa da shanuna da tumakina wadanda suka fi saukin kulawa fiye da ‘yan Nijeriya,” inji Buhari.

Buhari ya gode wa shugabannin kasashe da wakilan da suka halarci taron rantsar da Tinubu bisa goyon bayansu, ya kuma yi musu fatan alheri.

“Masu girma shugabanni da gwamnatocin jihohi da wakilansu, na gode muku matuka, kuma ina yi muku bankwana da kuma fatan alheri.

Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa da Shugaban kasan Ghana, Nana Akufo-Addo da Shugaban kasan Saliyo, Julius Maado Bio suna daga cikin wadanda suka halarci bikin rantsar da Tinubu.


Kalli Video Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post