Rundunar Sojin Ƙasa Ta Nijar Ta Goyi Bayan Juyin-Mulkin Da Ka Yi

 Rundunar sojojin ƙasa Nijar a ranar Alhamis ta bayyana goyon bayan juyin mulkin da sojoji masu tsaron fadar shugaban kasar suka yi, in da ta ce abin da ta sa a gaba shi ne kaucewa tada zaune-tsaye a kasar.

Alfijir Labarai ta rawaito a cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikata na sojojin ya sanya wa hannu, ya ce matakin ya zo ne domin kiyaye mutuncin shugaban kasar da iyalansa da kuma kaucewa “mummunan fada da ka iya haifar da zubar da jini da kuma shafar tsaron jama’a..

A baya dai shugaba Mohamed Bazoum da ministan harkokin wajen kasar, Hassoumi Massoudou sun bukaci dakarun dimokuradiyya a kasar da su bijirewa yunkurin juyin mulkin, yayin da jami’an kasashen yammacin duniya suka ce ba su san dalilin yunkurin juyin mulkin.

Sojojin sun ce a cikin wani jawabi da suka yi da daddare a gidan telebijin, an cire Bazoum daga mulki, an kuma dakatar da hukumomin jamhuriyar, wanda ke zama juyin mulki karo na bakwai a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka tun daga shekarar 2020.

Tun da farko sun datse fadar shugaban kasa a Yamai babban birnin kasar, tare da shugaban a ciki.


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post