Gwamnatin Nijeriya Za Tayi Watandar Naira biliyan 907 Ga Gwamnonin Kasar

 Gwamnatin Tarayya za ta yi wa kan ta, jihohi da ƙananan hukumomi watandar Naira biliyan 907.

HausaChannel Labarai ta rawaito hakan kuwa ya biyo bayan cire tallafin fetur da aka yi, har Gwamnatin Nijeriya ta tara Naira tiriliyan 1.9 a cikin watan Yuni.

Adadin yawan kuɗaɗen shiga a cikin watan Yuni ya zarce yawan adadin waɗanda aka tara a watan Mayu na bilyan 786.161.

Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Bola Tinubu, Dele Alake ya fitar da wannan sanarwa a ranar Alhamis.

Ya ce daga cikin ragowar kuɗaɗen, za a killace

Biliyan 790, saura kuma a zabtare haraji.”

Wannan gagarumar rabon da gwamnatin tarayya za ta yi, ta samo asali daga cire tallafin fetur.

A yanzu ganin al’umma ta shiga raɗaɗin tsadar rayuwa, gwamnati za ta raba tallafi ga marasa galihu.

Yayin da aka fara shirye-shiryen raba tallafin, Majalisar Tsara Tattalin Arziki ta ce rajistar sunayen masu karɓar tallafita ƙasa ba sahihiya ba ne.

Majalisar Tsara Tattalin Arziki ta Ƙasa, ta ce Gwamnoni su fito da tsarin cikakkar rajistar marasa galihu, domin wadda Gwamnantin Tarayya ke amfani da ita ba sahihiya ba ce.

Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo ya yi wannan bayani, bayan tashi daga taron su a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Alhamis.

Ya ce ya dace tallafin da za a fara rabawa ya kasance yana isa ga marasa galihu.

“Ya kamata mu faɗa wa kan mu gaskiya cewa babu wata sahihiyar rajistar marasa galihu a faɗin ƙasar nan.”

Ya kuma yi bayani cewa Gwamnatin Tarayya da Gwamnoni su fito da tsarin turawa marasa galihu alawus-alawus na rage tsadar rayuwa, gwargwadon karfin su.”

“Misali Gwamnonin da ba su biya kuɗaɗen famsho ba, su yi azamar biya waɗanda ba su biya ariyas ba, to su fara amfani da kuɗaɗen tallafin su bayar.

“Gwamnoni su ma tilas su rage almubazzaranci, domin a halin yanzu babu wani dalilin da gwamna zai fita da tawagar motoci 20.

“Ya kamata a cikin wannan halin a yi abin da ke daidai da talaka.”


Kalli Video Kaitsaye Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post