Yadda Kamfanin UK ENTERTAINMENT Ya Shirya Sabon Fim Mai Dogon Zango

 Mun shirya Fim din FATAKE ne domin Hausawan fadin Duniya, ba iya kacin Kano da Nijeriya ba.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban Kamfanin UK Entertainment Mal Umar Sani Lawal (Umar Uk) a tattaunawar da yayi da Jaridar kan sabon shirin kamfanin nasu mai dogon zango.

U K ya bayyana cewar duba da takaita tunani waje guda da yawancin yan uwansa masu shirya Fim suke yi, ya sa suka yi dogon nazari wajen samar da wannan Fim mai dogon zango da za su karade kasashen Afirka ana shirya shi, wato Fatake.

Ya kara da cewa duba da mahimmancin al ada da dabi un kowane rukunin da Hausa suke, shi ya saka duk kasar da suka je domin daukar wannan shiri muke amfani da jarumai na wannan ƙasar domin samun abinda ake bukata irin na wannan yankin.

Kalli Episode 1 Anan👇



Umar ya kara da cewar sun kalli abubuwan da ke saka Hausawa barin kasashensu na asali, wanda ya hada da kasuwanci, neman ilmi, rigimar sarauta, da sauransu.

Wadannan dalilai ne ya saka suka kulla zaren labarin nasu akan haka, wanda za a ga an fara da asalin in da Hausawa suke Nijeriya da Nijar daga nan mu kayi Ghana sai Nijar, Mali sai Kamaru, kuma dukkannin kasashen nan mun karaɗe ko ina a cikinsu duba da yan bambamcen karin harshe da ake samu.


Da wadannan kadai za a ga an samu bambanci da yadda muke gabatar sauran shirye shiryen fina-finanmu a baya. In Ji Umar U k


Hakazalika mun kalli yadda Fataken da suke gudanar da al amuransu da kuma an kulla abinda matasan zamanin nan ke bukata, wato soyayya tare da Nishadantarwa.


Kai ko ba a gaya maka ba, daga jin sunan Fatake kasan akwai magana kunshe ciki.

A yayin walimar da kamfanin suka hada don kaddamar da sabon shirin, an samu halartar jagororin gwamnatin jihar Kano irin su shugaban ma aikantan fadar Gwamnatin jihar (Chief of Staff) Alhaji Shehu Sagagi da sauran jagororin gwamnati.

Sai manya manyan jaruman masana antar da masu shiryawa da masu bada umarni da sauran jama ar Kannywood

U K ya bayyana cewar duk wanda yake da bukatar kallon fim din Hausa da asalin Hausawan kasashen Afirika sai ya tara ranar 2/7/2023 a tashar Gaskia Tv Plus akan tauraron dan adam karfe 8 na dare agogon Ghana sai karfe 9:00 na dare agogon Nijeriya da Nijar.


Kuma ita wannan tasha ta GASKIA

TV da GASKIA PLUS s kyauta ce ake kallonsu a duk inda kake a adireshin

  • Satelite: badr7 @ 26°E
  • Frequency: 11010
  • Symbol rate: 27500
  • Polarisation: Vertical



Baya ga nan akwai tashar youtube dinmu mai suna UK Entertainment ko Gaskia Tv YouTube itama zamu dora muku wannan shirin Fatake akwai baya ga fina-finanmu da za a iya samu a ciki.

Wato duk masu bibiyar shirye shiryen kamfanin mu sun san dama irin ingantattun fina-finan da muke kawo muku, ga kuma wanda bai san fina-finanmu ba, kafin wannan ranar su garzaya su gane wa idon su.


Post a Comment

Previous Post Next Post