Fadan Yan Bindiga Sbd Bazawara yajawo Mutuwar Mutane 64 a Zamfara

 Al’ummar garin Mutunji a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya suna cikin halin zulumi da tashin hankali, bayan asarar rayuka mafi muni da garin bai taɓa ganin irin sa ba.

Rahotanni daga garin sun ce a ƙalla mutum 64 ƴan garin ne suka rasa rayukansu bayan da wani jirgin soja ya jefa bam a wani waje da ƴan bindiga suka yi mafaka.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa saboda tsaro ya tabbatar wa BBC cewa dukkan waɗanda suka mutun maza ne, mafi yawan su ƙananan yara, sai kuma matasa da tsofaffi.

“An yi asarar rayukan da ba a taɓa samun yawan hakan ba a rana guda a garin namu kuma baya ga wadanda suka rasa rayukansu da dama sun jikkata,” ya ce.

Ganau din wanda shi ma ya rasa ƴan uwansa da dama, ya ce an kai waɗanda suka jikkatan asibitin garin Dan Sadau da na Gusau ana duba su.

“Mutum 17 suna asibitin Dan Sadau su kuma 12 da suka fi jin munanan raunuka suna asibitin Gusau duk ana kula da su.


Faɗa a kan bazawara

Jama’ar garin na Mutunji sun ce kwana shida da suka wuce ne wasu dabobin ƴan bindiga biyu a garin Randa suka yi rigima a kan wata bazawara “da kowa ke so”.

A kan hakan ne aka samu hatsaniya tsakanin su a cikin daji har aka kashe mutum biyu.

Ganau ɗin nan ya ce wa BBC “to daga nan ne sai wani babban ɗan bindiga ana ce masa Damina, ya ce ai mutanen garin ne suka kashe masa yara a don haka sai ya kwashe ƴan garin har mutum 174, a ciki ya kashe mutum 20.

“A yanzu haka kuma wasu fiye da 150 suna hannunsa. Kuma majiyoyi masu ƙarfi sun shaida mana cewa kisan gilla ya yi wa mutane 20 ɗin.

“Bayan nan ne sai Damina ya ce wa mutanen garin Randa ya yi binciken da ya kamata ya yi kuma ya gano mutanen garin Malele ne suka kashe masa yaran,” ya ce.

Jama’ar garin sun kuma ce hakan ya sa aka kai wa mutanen Malele hari, a yayin hakan ne kuma suka yi wa sojoji kwanton ɓauna har suka kashe tara daga cikin su, suka kma jikkata huɗu da a yanzu haka suke asibitin Dan Sadau.


Wata majiya daga rundunar sojin ta tabbatar wa BBC cewa sojoji 12 ne suka mutu amma su ma 'yan bindigar da dama sun rasa rayukansu.

Wannan abu da ƴan bindigan suka yi ne ya sa sojojin suka nemi ɗauki daga sojojin sama, su kuma ɓarayin lokacin suna neman mafaka sai suka fada garin garin Mutunji.

Post a Comment

Previous Post Next Post