Abin da 'yan Najeriya ke son sani kan badaƙalar kudin harajin bankuna

 A Najeriya, batun harajin da bankuna ke cire wa wadanda suka yi amfani da asusun ajiya wajen tura kudi ko cirewa na ci gaba da janyo cecekuce.

A makon da ya wuce ne kwamati na musamman da Shugaba Muhammdu Buhari ya kafa domin gudunar da bincike kan cajin cirewa da ajiyar kudi a asusun banki ya yi zargin cewa wasu hukumomin da binciken ya shafa suna kokarin hana shi yin aikinsa, da kuma hana shi ya mika wa Buhari rahotonsa.

Sai dai sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twitter, mai magana da ywun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya ce lokacin da Shugaba Buhari ya karbi ragamar kasar a shekarar 2015 ya samu wannan doka ta cajin kudin haraji da bankuna ke karba idan an tura kudi, amma kuma ba a aiki da ita yadda ya kamata ba.

"Lamarin ya kara tabarbrewa, bayan da aka smu wasu da suka hada kai da hukumar sakon gidan waya wato NIPOST, inda aka yi zargin an adana kudin cikin aljihunsu bayan wata hukumar gwamnati ta zuba zunzurutun kudi har naira tiriliyan 20 tsakanin shekarar 2013 zuwa 2016, tare da ikirarin za a iya gano kudin tare da zuba su a lalitar gwamnati," a cewar sanarwar.

Kwararrun da za su nemo kudden sun bukaci a ba su kashi 7.5 cikin 100 na kudaden karkashin sa idon tsohon Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugabn Kasa Marigayi Malam Abba Kyari, kamar yadda ya rubuta wasika a watan Maris na 2018 kan korafin rashin yin abin da ya dace daga wadanda aka dora wa alhakin bincike kan batun."

Sanarwar ta ci gaba da cewa Abba Kyari ya kuma bukaci a dakatar da kwamatin kwararrun masu ba da shawarar lalubo bakin zaren, inda aka karkatar da kudaden. Kan haka ne su kuma suka kai karar gwamnatin Najeriya.

Batun har gaban kuliya ya je kuma bayan tsawon lokaci ana tattaunawa a kotun, gwamnatin Najeriya ta yi nasara.

Bayan haka ne kuma aka sake mayar da batun gaban majalisar dokoki, tare da yi wa dokar kwaskwarima da kuma cire NIPOST daga karbar harajin.

"Wannan dalili na rasa samun kudaden da kwamitin ya yi, shi ne suka fara ta da jijiyar wuya da daukar sabon salon yi wa gwamnatin Najeriya barazana a fakaice," in ji gwamnatin Najeriya.

Garba Shehu ya ce: ''A baya-bayan nan sun sake dawowa, suka yi amfani da Honrabul Gudaji Kazaure da aniyar wai za su sake bibiyar batun kudin harajin da bankuna ke cire wa abokan hulda da kamfanoni, sun kuma nada wani shugaban kwamati yayin da shi kuma Kazaure yake sakatare.

"Bayan dawowar shugaban kwamitin da Marigayi Abba Kyari ya rusa a wasikar da ya aike wa shugaban kasa a watan Maris na 2018, a matsayin shugaban sabon kwamitin, Shugaba Buhari ya janye amincewar da ya bai wa kwamatin na aikin tun farko.''

Gwamantin Najeriya ta damu kan sanya sunan Alƙalin Alaƙalai Mai Shari'a Olukayode Ariwoola a matsayin mamban kwamatin, da kuma dan majalisa mai ci a matsayin sakatare, wanda a cewarta hakan ya saba wa sashe na 5 (1),(a) da (b) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 (da aka yi wa kwaskwarima).

"Kwamatin ya rasa damar yin aiki tun daga lokacin da Shugaba Buhari ya dakatar da shi. A dan tsakanin nan, ana ta cecekuce da muhawara kan ko kwamitin na da sahihanci ko a'a, ko ya ci gaba da aiki ko a'a.

''Mutane na da damar fadin abin da suke so, hakan ba zai sauya matsayar kundin tsarin mulkin Najeriya ba, kuma shugaban kasa na da karfin ikon nadawa da sauke wasu a kungiyance kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba shi iko."

Garba Shehu ya ce ya yi mamakin yadda dan kwamitin kuma mamba a jam'iyyarsu, Honabul Gudaji Kazaure ya nemi tsoma shi cikin danbarwar.

"A bayyane take karara kwamitin da ke ikirarin kudin da ya kai naira tiriliyan 89 na kudin harajin da ake cirewa 'yan kasa ba gaskiya ba ne, lissafin dokin rano ne," in ji shi.

A shekarar 2016 ne kwamitin ya ce an karbi naira tiriliyan 20 amma baki daya kudin da bankin ya sanya bai kai rabin tiriliyan 89, ya kuma so yin shiru amma sai ya ga Honarabul Gudaji na son janyo shi cikin batun.

"Batun ba shi da tushe ballantana makama, kuma kudaden da ake magana a kai sun yi yawan da hankali ba zai dauka ba, sannan shi kansa Babban Bankin Najeriyar [CBN] ba shi da irin kudaden."

Cikin wata hira da ya yi da BBC Hausa, ɗan majalisar Wakilai Muhammad Gudaji Kazaure daga Jihar Jigawa ya ce kwamatinsa da Buhari ya kafa ya gano CBN ya tara naira tiriliyan 89 daga kuɗaɗen caji a asusun bankuna na ɗaiɗaikun 'yan ƙasa.

Honorabul Kazaure ne sakataren kwamitin kuma ya shaida wa BBC cewa: "Kwamitinmu ya gano naira tiriliyan 3.9, kuma ya yi kokarin shiga babban bankin Najeriya domin gano inda wadannan kudaden suke cikin asusun ajiya uku."

Kazalika, Gudaji ya ce lallai akwai kudi naira tiriliyan 89, kuma "suna iya biyan bashin da ake bin Najeriya kaf!"

Ya nemi a cire gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele domin yana mai cewa "idan yana kan mukaminsa ba zai bari mu gudanar da aikinmu na binciken CBN ba. Ba zai bari ba."

Martanin da ya mayar wa Garba Shehu cikin wa sanarwa da ya fitar ranar 11 ga watan Disamba, Gudaji Kazaure ya ce Buhari ne da kansa ya naɗa 'yan kwamatin.

"Don kore dukkan shakku, Shugaban Ƙasa ne ya umarci kwamatin ya yi aiki da DSS kuma da kansa ya ce kar wani hadiminsa ya shiga lamarinmu," a cewarsa.

"Da a ce kwamatin ba na gaskiya ba ne, me ya sa gwamnan CBN yake haɗa kai da na kusa da shugaban ƙasa don su hana ni ganin sa? A matsayina na ɗan Najeriya, babu wata doka da ta hana ni yin aikin da shugaban ƙasa ya saka ni."

Post a Comment

Previous Post Next Post