Nasamu Juna Biyu Ummi Rahab Hakan Yajawomun Farinciki Awajen Lilin Baba

 Na Samu Juna Biyu, Cewar Tsohuwar Jarumar Fina-finan Kannywood, Ummi Rahab matar Lilin Baba

Matar mawaƙi, furodusa kuma jarumi Shu’aibu Ahmed Abbas (Lilin Baba) kuma tsohuwar jarumar Kannywood, Rahama Saleh Ahmed (Ummi Rahab), ta bayyana cewa ta samu ciki.

 Ummi ta ba da wannan sanarwar ne a Instagram, inda ta wallafa hoton ta sanye da jar atamfa, ta na zaune a kan kujera ta na murmushi. A saƙon, da ta rubuta da Turanci da manyan baƙaƙe: 'I’m pregnant' wanda Majiyar Focus News Hausa, mujallar Fim ta fassara da, “Na samu ciki” Jarumar mai ritaya Saboda Auren datayi tayi kira ga masoyanta da su tayata murna, har ta yi alƙarin za ta ba da tukwicin katin waya ga mutum 50 na farko da su ka tura saƙon murnar a ƙasan hoton nata.

Haka Kuma Tacigaba dacewa: “Idan na samu ‘comments’ ta hanyar rubuta Congratulations a ƙarƙashin wannan hoton, zan ba da kyautan katin Waya … ga mutane 50 Sai dai bata faɗi ko katin nawa ɗin za ta ba kowane mutum ba.

Haka kuma matar ta Lilin Baba ba ta bayyana ko cikin nata ɗan wata nawa ne ba. Dubbanni Kuma Ɗimbin masu bibiyar ta a Instagram sun taya ta murna tare da taya ta fatan alheri.

Ita dai Ummi, an ɗaura auren ta ne da Lilin Baba a ranar Asabar, 18 ga Yuni, 2022, a Tudun Murtala, Kano, a kan sadaki N200,000.

Jarumi Ali Nuhu, wanda shi ne waliyyin ango, shi ne ya karɓi auren.


 Dohaka Mai Karatu Kanada Damar Tofa Albarkacin bakinka/ki Akasan wannan Rahoton, Kuma Don Allah Atayata Murna da Farinciki da Karuwan da ta samu Arayuwarsu ta Aure da Angonta Lilin Baba, please a Tsarkake Harshe/Rubuta Banda cin zarafi ko Hassada da kyashi kokuma Son Zuciya.. 

Post a Comment

Previous Post Next Post