Raba Raini Fassarar sultan Indian Hausa 2022

   RABA RAINI (Sultan)


Daga cikin ďakin ta jiyo muryar dattijon wanda ya bata tabbacin shima yana ciki. "Toh ki ce an gode, je ki ďauki naira ashirin a saman tagar ďakina kiyi gaba.
A hankali ta sauke ďankwalin da aka ďaure kayan a ciki ta kwance ta fito da sababbin samirun tuwo da miya ta cire ďankwalinta tace "Nagode BAFFA, Allah ya saka da alkhairi." Ta ďauki ashirin ďin ta fita cikin k'unan rai.
A hanyar da zata sada ta da kofar gida taci karo da su Husna rik'e da manyan kuloli suna tafe suna nishi da kyar, rab'ewa tayi ta basu guri dan su wuce, suna karasowa dab da ita suka kwashe da dariya haďe da faďin "
Nadiya roba-roba. Badariyya ta ajiye kular hannunta ta shafi kayan jikin Nadiya tace 
"Kaiii!! Wannan ba roba bace rai fess ce."
Suka sake tintsirawa cikin shakiyanci suka ce "Su Nadiya bana an samu canji, daga atamfar roba zuwa shaddar roba.

Cikin sanyin jiki tayi gaba tana jiyo ihunsu har suka shige cikin gidan. Tana fita tayi tafiyar minti biyar sannan ta isa titin da zata roki masu mota su ďauketa da naira ashirin ďin da aka bata, dan in tace zata tafi gida a kafa sai ta kai yamma saboda nisa, zuciyarta cike take da mamakin yadda zumuncin zamani ya koma. tun tana karama ta ga mahaifiyarta na fuskantar irin waďannan wulakancin saboda kasantuwarsu talakawa, sau tari takan tambayi mahaifiyarta anya Baffa ne ya haifeta kuwa?

Acikin gidan kuwa, su Husna na shiga babu ko sallama suka faďa ďakin, zabura Baffa yayi ya sakko daga kan gado yana faďin. "Lale da matana, lale-lale. Badariyya ta faďa jikinshi tana faďin "Kakus, ina barka da Sallah na? Cikin rawar jiki yasa hannu a aljihu ya ciro yan ďari biyar-biyar sababbi ya k'irga goma ya bata, yatsina fuska ta yi tace Haba kakus, dubu biyar fa ka bani, ni gaskiya sunyi min kaďan Pizza kaďai zanci da su. Washe baki ya yi yace. To yar lele, an gama. Ya karo mata wasu biyar ďin ta mike a jikinshi babu ko godiya sai ma faďin Ko kaifa, ai da na sake ka yanzun nan, Husna ta matsa kusa dashi tace Saura ni kakus. Dubu goman itama ya bata saboda yasan sakon barka da sallan shi na tafe don tun safe y'arshi mafi soyuwa a gareshi ta kirashi tace zata aiko MUSADDIQ da sak'o, yasan sakon bai wuce na kuďi.

"Ina yayanku? Ko ba tare kuka zo ba?" Baffa ya tambaya yana gyara aljihu. Badariyya tace Ka ji kakus a kofar gidannan fa muka sameshi, yana fita muna shigowa dan ya riga Nadiya fita ma. Kallon mamaki yayi musu yace Aiko bai shigo ba. Goggo ta rufe kular da ta bude ta ce Kasani ko ya manta da wani abu ne? Hakane kuma. Ya faďi tare da basar da maganar. Nan suka hau hira da ciye ciye, sun ma manta da samirun tuwon da Nadiya ta kawo saboda sunsan babu wani abun arziki a ciki.

Zaune take tayi tagumi tana jiran shigowar Nadiya dan tasan in Allah Ya yarda zata samu ko ďari biyar ce a gurin su Baffa na barka da sallah, Zainab ce ta taso rike da robar abinci tace Mamma zan kara abinci. Janyota ta yi jikinta tace Yi hakuri auta, yanzu Anti zata dawo har madara ma sai kisha in kinaso kinji? Gyaďa kanta tayi cikin murna ta kurawa kofar gidan ido tana jiran b'ullowar yayarta.

A gajiye ta shigo gidan ta nemi guri ta zauna tana maida numfashi, da sauri Zainab ta mike ta ďauko mata ruwa, karb'ar ruwan tayi haďe da janyota jikinta tace Kin ci abinci? D'aga mata kai tayi, "Eh naci amma ban koshi ba. Mamma ta ce zaki kawo kuďi a siyo min madara. A hankali ta ďago jajayen idanuwanta ta sauke kan mahaifiyarta, kallon tausawa juna sukayi sannan suka kau da kawunansu, cikin sark'ak'ak'k'iyar murya Nadiya tace "Mamma na kai musu, Baffa ya bani naira ashirin, ki tayani yi mishi godiya dan ya taimakamin, da a kafa zan dawo gida. Cikin b'oye b'acin rai Mamma tace Kai madallah!! Allah ya biyashi da aljanna, gaskiya naji daďi, tashi maza kije kiyi sallah. Tana kokarin mikewa taji anyi sallama, juyowa tayi haďe da amsa sallamar, suna haďa ido tayi saurin kau da kanta.


Mamma ta mike cike da murna tace 

"Maraba da Musaddiq, yanzu kake tafe? Eh Mamma ina wuni. Haba dai daga tsaye? Ta faďi haďe da shimfiďa dadduma. Zama yayi yana sosa k'eya suka gaisa sosai, kuďi ya zaro a aljihunshi kusan dubu dari biyu yace gashi inji mummy tace a kawo muku" bai jira jin me zata ce ba ya ajiye kuďin ya fice daga gidan da sauri dan yasan in ya daďe a gidan to asirinshi zai tonu. Kasa tab'a kuďin tayi saboda firgici Kai anya Musaddiq yaji inda aka aikeshi da kyau kuwa? Wannan kyautar tayi yawa dan tsakanin ta da yar uwarta bai wuce kyautar dubu biyar Nadiya mik'o min wayar can" tace tana mai nuna ma nadiya wayar, da sauri ta ďauko ta mik'a mata. Hannu na rawa ta fara neman lambar yar uwarta, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta ďaga cikin isa da tak'ama, murya na rawa Mamma tace "ina yini Hajiya lafiya kadai tace murya can k'asa, bata damu da amsawar ba dan in da sabo ta Saba, sai ta cigaba "yanzu Musaddiq Ya kawo min sak'o shine nace bar.

Dakatar da ita tayi ta hanyar cewa "ina da abin yi Suwaiba nasan godiya kika kira kiyi, bakomai yiwa kai ne" tayi saurin kashe wayar, cikin mamaki ta ajiye wayar tana duban kuďin zuciyarta cike da farin cikin yar uwarta ta fara sanin muhimmancin zumunci.

Musaddiq na fita ya nufi motarshi ya kashe wayoyinshi ya ta da motar yayi gaba yana nazarin yadda zaiyi ya fahimtar da mahaifiyarshi da kakanninshi muhimmancin zumunci,

A kullum yana mamakin yadda zumuncin zamanin yanzu ya zama sai in kana da kuďi, 
yana takaici matuka saboda irin wulak'ancin da Mamma suwaiba da ya'yanta ke fuskanta saboda kawai basu dashi, bashi da wani burin da ya wuce yaga kan zuri'arsu ya haďu, Mai shi ya taimaki mara shi, amma kullum abun k'ara lalacewa yakeyi saboda masu shi ďin basa taimakawa na jikinsu saidai na neman suna..

Post a Comment

Previous Post Next Post