Lokacin da ya ce zai Aure ni - sai da iyayensa suka lakada masa dukan Tsiya

 Bata taba tunanin zata je makaranta ba acikin rayuwarta kuma ta auri mutumin da take so, balle ma ta haifi 'ya'ya. (Ibeadua Judith Chioma).

  Tayi wannan tunanin ne saboda matar, Wacce Takeda shekaru 31, Tanada nakasa kuma iyayenta sun rasu tun tana 'yar shekara shida a Duniya.

Ibeadua Judith, wacca bata dade da kammala bautan ƙasa a Najeriya (NYSC), tace 'yan mata irinsu suna zuwa makaranta ne kawai idan ba su samu namijin da za su aura ba.

Lokacin Kafin Tayi Aure, da mijinta ya faɗa wa iyayensa niyyarsa ta auren Judith sai da suka taru suka lakada masa duka har ma suka raunata shi, in jita.

Ba da lalura aka haife ni ba'
Ina 'yar shekara huɗu na rasa ƙafafuwana kuma na gano ba zan iya tafiya ba. Ban san abin da ya faru ba, iyayena za su iya ba da labari amma kuma sun rasu tun ina 'yar shekara shida," kamar yadda Judith ta bai wa BBC Pidgin labarinta. Lokacin da iyayenta suka rasu, sai yayarta ta ci gaba da kula da ita kuma ta kai ta makaranta tun daga nazire har zuwa aji uku na ƙaramar sakandare.

"'Yar uwata ce ta ɗauke ni, ta ci gaba da koya min abubuwa. Da rarrafe nake zuwa makaranta da coci, na yi ta kuka ina tambayar Allah me ya sa ya yi ni haka cikin irin wannan halin," in ji ta. Gwara na mutu da na yi bara a kan titi in ji gurguwa mai sana'ar dinki

ALokacin da take JSS1 ne wani malamin Kirista ya saya mata keken guragu. Bayan ta kai JSS3 kuma sai shugaban makarantar tasu yaba da shawarar a kai ta makarantar masu buƙata ta musamman. A nan ne rayuwarta ta fara kyautata. Ta haɗu da mutanen da rayuwarta ta fi tasu dama-dama, a nan ɗin ne kuma ta haɗu da mijin da ta aura.


Duk da wuyar da mijina ya sha bai guje ni ba

Sun haɗu da mijinta gaba da gaba a karon farko bayan sun shafe shekara biyu suna magana ta wayar salula. Damuwar mijin nata da ɗan uwansa da ya haɗa su ita ce; ta yaya za ta iya aikin gida da haihuwar yara da kuma karatu bayan iyayensa sun ƙi amincewa da auren.

Har ma sai da wasu 'yan uwansa suka doke shi. Amma a yanzu tana godiya da farin cikin cewa mijin nata bai guje ta ba. Lokacin da mijina ya ce zai aure ni mahaifiyarsa ta kira mutane don su taimaka mata a zane shi saboda shi kaɗai ne ɗanta namiji. Suka zane shi sosai har suka raunata shi, in ji ta.

Amma duk da wahalar da ya sha bai guje ni ba.

Ta ƙara da cewa abin da suka fi damuwa da shi shi ne yadda za ta ɗauki ciki, idan ma za ta ɗauka ɗin. Yanzu haka ta haihu ba cikin sauƙi ba tare da wata tiyata ba.

Aure, karatu da sauran ƙalubala

Bayan Sunyi Aure, mijinta ya shawarce ta ta ci gaba da karatu. Ta yi aure ne tana ajin ND 2 kuma tana da ciki.

Ta karanci fannin koyarwar kwamfuta wato Computer Education a kwalejin kimiyya, inda ta kammala bayan shekara shida saboda annobar korona.

"Na samu gurbi a 2015. Na yi karatun shekara shida saboda annobar korona.

Duk da cewa burinta shi ne ta karanta harkar likitanci, amma lokacin da muka fara karatun sai suka ce ba sa ɗaukar masu nakasa a sashen likitanci.

Post a Comment

Previous Post Next Post