Yan Ta'adda Sun Rufewa manoma Hanya a Zamfara: Nigeria

 Wasu manoma acikin jihar Zamfara wacce ke arewacin Najeriya, gawani daga Cikinsu mai suna Malam Sama'ila Muh'd, wanda ƴan bindiga suka datse hannayensa biyu ya ce ya miƙa lamarinsa ga Allah kuma Allah saka masa.


Manomin dayake zaune a ƙauyen Walu a ƙaramar hukumar Kauran Namoda ya bayyana cewa shi da ƴan uwansa sun ci karo da ƴan bindigan ne bayan sun fatattaki wasu ɓarayi da suka je satar kaji a gidansu kusan sha biyun dare, fiye da mako guda da ya wuce.

  Malam Sama'ila ya shaida wa BBC cewa bayin Allah ne suka shiga gidanmu, suka kama kaji sai suka fita, sai na ji sun shiga wajen ƙanina suna bugunsa, sai na ce jama'a kun ji suna bugun auta, ku taho mu je gare su.

  Ashe sun ji, sai suka tsallaka katanga suka fita da gudu, sai muka bi su, da muka bi su sun yi nisa sai nake cewa ƙannena su dawo tun da sun tafi su dawo, ashe waɗannan masu bindiga sun koro bisashe (dabbobi).

Ya ce ƴan bindigar sun tsare su tare da tambayarsu "kai me kuke yi nan", sai na ce "yara na kira su dawo, magana ta ƙarshe sai ya ce masa me kuke jira? Kawai sai na ji abin da suke yi a wajen sai na ji sara da adda suka sauke mana hannaye gaba ɗaya. Manominya ce ba ƴan bindigar da suka je satar kaji ba ne suka yi musu aika-aikar sai dai ya ce ƴan bindigar suna yawan zuwa wajen kuma suna sace musu kayayyakinsu.

Ya ƙara da cewa har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da taɓarɓarewa a yankinsu duk da cewa jami'an tsaro na iya ƙoƙarinsu amma "abin ne ya yi yawa.

A cewarsa, yana samun sauƙi kuma likitoci suna kula da shi sosai inda ya ce "ko abinci sai an ɗauka an bashi.

Post a Comment

Previous Post Next Post