Hawa Jirgin Sama Yazama Bala'i ga masu Tafiye-Tafiye

 Fasinjojin hawa jiragen sama na Najeriya na kokawa kan yadda kamfanonin jirage ke tsauwala kudin tikiti acikin ƙasar.

Wannan kari ya zo ne sakamakon ƙarancin man jiragen sama na JetA1 da ƙarancin kuɗaɗen ƙasashen waje domin sayayyar kayayyaki masu nasaba da zirga-zirgar jiragen.


Karin kudin jirgi ya sa farashin tikiti kan kai har sama da naira 100,000, misali daga Legas zuwa Kano da sauran birane, lamarin da ya tilasta wa fasinjoji komawa bin mota. Amma fasinjojin na cewa hakan ya zama gaba kura baya sayaki sakamakon masu garkuwa da mutane da suke tare hanyoyin ƙasar.

Da yawa daga cikin ‘yan Najeriya, hatta wadanda ake kira matsakaicin samu, na cikin wani mawuyacin hali na ko dai ɗaukar kasadar tafiyar mota, ko kuma su yi hakuri da karin kudin tikitin su bi jirgin sama.

Sai dai a wasu lokutan bin jirgin da kudinka ma kan zama tashin hankali, saboda yadda kamfanonin ke yawan soke tafiya bayan mutane sun je filin jirgin saman, ko kuma a ɓata lokaci sosai kafin a tashi.

Rahotanni sun nuna cewa kudin tikitin jirgin sama a halin da ake ciki daga Kano zuwa Abuja ya kan kai kusan kai Naira 160,000 idan a kwatanta da ‘yan kwanakin baya da yake kan naira N95,000. Sannan idan aka kwatanta da wata uku da suka wuce za a ga cewa ƙarin ya shallake hankali, saboda a farkon shekarar nan tikiti bai cika wuce naira 35,000 ba.

Bincike ya nuna hakan ba zai rasa nasaba da sanarwar da gwamnati ta bayar na cire tallafi kan harkar jirgin sama ba a makon jiya.Wannan ya kara sanya ana samun jinkiri da soke zirga-zirgar jiragen sama a kasar.

Muna cikin wahala

Wasu daga cikin fasinjojin da BBC Hausa ta ji ta bakinsu sun bayyana cewa matsalar ababen hawa da ta hanyoyi a kasar, musamman na jirgin sama a yanayin da ake ciki na dagula musu al’amura.

"A gaskiya sai dai mu ce Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. A da mukan hau jirgi mu yi tafiye-tafiyenmu, amma a yanzu ba zai yiwu ba, kuma hanyar motar ma ta gagara bi," a cewar Alhaji Abubakar, wani mai yawan bin jirgi don hidimomin kasuwancinsa.

Ya ƙara da cewa da mai kudi da talaka kowa yana ji a jikinsa. Ya ce: “Idan ka je iyafot a da sai ka ga kamar mutum 100 da za su hau jirgi amma a yanzu da wuya ka ga 30.” Shi ma wani fasinjan da da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce a halin da ake ciki gaba kura baya sayaki ne.


“Ka hau mota ka sayar da rai, ka bi jirgi kuma babu kudin. “Gaskiya idan dai tafiya ba ta zama dole ba ina shawartar mutane da gara su haƙura da ita kawai,” ya ce.

Akwai dubban ‘yan Najeriya ko fasinjoji na cikin gida da tuni suka yanke kaunar hawa jirgin sama anan kusa inda suka koma tafiya ta hanyoyin mota.

To sai dai a yanayin da a yanzu ake ciki na tare hanyar mota saboda masu garkuwa da mutane da ƴan bindiga a arewa da kuma na ‘yan kungiyar IPOB a kudu sun sa bin hanyoyin ma babu dadi. Baya ga wadannan dalilai akwai kuma wasu manufofi na gwamnatin kasar da suka ci karo da harkokin kamfanonin jiragen sama a kasar.

Alhaji Abdulmunaf Musa shi ne shugaban masu kamfanonin jiragen sama a Najeriya, ya ce wasu daga cikin manyan dalilan da yasa aka kara kudin jirgi sun hada da karancin kudin kasar waje da karancin man jiragen sama na JetA1 da kuma tsadar sayen sassan jikin jirgin sama daga kasashen waje.

Sai dai ya ce farashin jirgi daga wannan jihar zuwa waccar ya dogara da lokacin da fasinja ya yi cinikin samun tikitin.


An bar shiri tun rani

Tun ba yau ba masana kan harkokin jiragen sama a kasar ke kira domin lalubo hanyoyin warware wannan matsala da a yanzu ta zama gagarabadau.

Tsohon manajan daraktan hukumar kula da sararin samaniya ta NAMA, kuma ƙwararre ne a fannin tuƙin jiragen sama, Kyaftin Ado Sanusi ya ce tun farko ba a shawo kan matsalar da wuri ba ne. “An sami kuskure tun daga farko lokacin da man jirgi ya fara tashi, kuma ƙungiyar jirgin saa ta je wajen gwmanati don a talkfa musu.

“A lokacin gwamnati ta tallafa musu kiuma ba a samu karin kudin jirgin ba. Amma kuma duk sati biyu zuwa uku ana samun ƙrin farashin kuɗin man jirgin., kuma gwamnati ba ta samar musu man yanzu. “Don haka dole su saya da tsada yadda ake kawo shi. Shi ya sa za a duk mako sai an kara kudin. Kyafin Sanusi ya ce mafita ga wannan lamari ita ce a samu man ya wadata kuma ya zama ana samun sa da rangwame.

“Sannan gwamnati ta dinga tallafa wa kamfanonin jiragen ta wajen dauke musu haraji da kuma samar musu dala da sauki don sayo kayayyakin da suke bukata. “Kuma idan matatar man Dangote ta fara aiki ma to komai zai yi sauƙi,” a cewarsa. Wani bincike da na gudanar ya gano cewa matsalar tashin kudin jirgi ba ta tsaya a Najeriya ba kawai.

Su ma kamfanonin kasashen waje sun yi gargadin halin da ake ciki cewa yana iya kara tabarbarewa da kuma sanya matafiya a Najeriya biyan sama da kudin da suka sani a baya. Sai dai sun ce idan gwamnatin tarayya ta shigo domin daidaita makudan kudaden kamfanonin kasashen waje da suka kai dala miliyan 450 da suka makale a kasar a iya samun sauki.

Masana tafiye-tafiye ta jiragen sama sun ce akasarin kamfanonin na kasashen waje sun daina siyar da tsohon tikiti akan farashi mai rahusa a Najeriya, lamarin da ya bar matafiya da zabin biyan makudan kudade. To sai dai daga bangarensu akwai wani dalili da ya banban da na kamfanonin jiragen sama na Najeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post