Batan Kai Fassarar Sultan Sabuwar Fassara Indian Hausa 2022

   BATAN KAI (Sultan)


   K'arfe takwas na dare take takawa a hankali cikin layukan unguwar tasu,iskace irin ta sanyi ke kadata hagu da dama,tana kuma kada dan yalolon hijabin dake mannewa a jikinta kasancewarsa na roba,uwa uba tsufa da shan jikin da yayi wanda ya rage kaso hamsin cikin dari na kaurin asalin yadin.

   Kusan hankalinta bai jikinta, tayi nisa qwarai cikin tunani wanda har hakan yasa ya bata damu da wanda ke gabanta ko bayanta ba bare gefanta, tunanin nata dukka yana kan qannenta data bari wuni guda sur yau a gida, batasab me sukaci ba yaudin,ko umna kattume ta basu abinci?, ko yauma tayi musu irin halin nata data saba, da yunwa suka kwanta ko kuwa sun qoshi?,duka ire iren abinda yake damunta kenan tunda ta fito daga gidan umma luba takamo hanyar gidan nasu, wanda duk da yake cikin unguwa daya suke amma akwai 'yar qaramar tazara a tsakaninsu.
   Hannu tasa tadan share kyakkyawar fuskarta da takejin qurar hazo samanta,wanda hakan ita bai dameta,takan dauki lokaci mai tsaho kafin ta sanya mudubi gaban idanunta takalli fuskarta,duk wata halitta takyau da Allah yayi mata baiwarsa saidai tajita daga bakin mutane,bata taba tsaiwa ta kalla ba bare ta tantance,hasalima bata da wannan lokacin ko kadan a rayuwarta.
 Yammata daga ina haka? Ta tsinci muryarshi daga bayanta,gabanta ne yayi wani mummunar faduwa, tun kafin tajuya tasan waye,ko kusa ko alama ta tsani duk wani abu da zaya hadata dashi, bata qaunar tarayyarsu ko alaqa dashi, hakanan ta tsani irin abinda yake mata, ita kwata kwata bata sanya kanta cikin jinsin mata bare har wani yace zai damu da rayuwarta da sunan soyayya,a wannan halin da take ciki?,tana ganin babban zaluncine a gareta wani dan adam ya takura mata da kalmar so ko qauna.

  kalmace dako sau daya bata taba magana akanta ba walau a zuci ko a fili,a karan kanta ko ita da wani, towai dawa ma zatayi zancanta?,wa take dashi, bata da kowa bata da abokin magana shawara ko tattaunawa,bata da wanda zata gayawa shawara ko damuwarta face 'yan qannenta,wanda su kansu basu gama fuskantar rayuwar ko matsalarsu ba bare su fuskanci ta wani.

  Koda tana da wani gata ko wani tsayayye,tana ganin babban zunubine a shekarunta qwalli goma sha biyar kacal ta jefa kanta a wannan layin.

   Tana tsaka da wannan tufka da warwara yasha gabanta,yaja birki yana kallonta, tsantsar baiwar kyawun da Allah ya mata ta bayyana tarwai a dan ragowar hasken farin wata wanda hazo yayi nasarar dakushe kaso mafi yawa na hasken nashi, qare mata kallo yaci gaba dayi yana jin yadda yake sonta cikin zuciyarsa, bilkisu nada wani irin kyau mai sanyi da shiga zuciya, hakanan komai nata mai kyaune, kama daga kallonta, tafiyarta da maganarta, hatta da shurunta ma,komai nata abun burgewa ne, duk da tarin talauci da fatara daya musu katutu kuwa,yasha rayawa a ranshi wannan da a gidan wadata take ba shakka ba qaramin haddasa fitina kyawun nata zaiyi ba,matuqar yasamu dukkan wani abun buqata da zai bayyana kanshi yadda ya kamata,ba kamar yanzu daya tabbatar da cewa duk da yadda yake ganin kyawun nata fatarar da suke ciki ta wawashi kaso mai yawa ta boye ba.

   Da wannan damar tayi amfani ta kewayeshi cikin matuqar sauri da wani irin hanzari tawuce,to ba ma'abociyar iya saurin bace ita,hakan yasa baiyi wani taku mai yawa ba ya cimmata,yayin da zuciyarta taci gaba da bugun uku uku,Allah Allah kawai take takai gida wannan qaramar alqar tasu ta yanke.

  Dab da dakalin qofar gidansu yake a zaune,shi daya da alama yaudin babu 'yan tayin hirar nashi duk dare da suka saba zaman kisan dabe,masu matattar zuciya kusan irin tashi,kuma 'yan amshin shatar nashi,hakan yasanya tasu tazo daya dasu sosai, Ke bilki, bilki!, zo nan" ta tsinci muryar mahaifin nata a sanda yana kwado mata kira a sanda take gab da shigewa soron gidan nasu.

  A matuqar sanyi ta sauya akalar tata zuwa inda yake zaune,ta gefen idanu tana iya hango sabi'u wanda yasamu wani waje ya lafe bai qaraso inda suke ba sakamakon ganin mahaifin nata da yayi zaune a qofar gidan nasu.

   A ladabce ta isa gabanshi kana ta durqusa da dukkanin gwiwoyinta,kanta na kallon rairayin dake shimfide gabanta, Gani baba sai yatashi yazauna sosai daga kashingidar da yayi,ya gyara hularshi dake niyyar zamewa tazauna sosai a kanshi Yauwa yafada yana sake gyara zaman rigar wuyanshi kamar wanda ya qwaci kanshi daga hannun 'yan dambe, Dama cewa nayi zan samu wani abune a wajenki?,yau natashi bani dako sisi wallahi,waccar kafirar kuma yau tsiyarta ta motsa ganin na tada sabon ginin dakuna,ta hanani abincin daren ma kwata kwata" wani dunqulallen abu mai tauri taji yazo mata iya wuya ya tokareta.

1 Comments

Previous Post Next Post